rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Falasdinawa Isra'ila Hakkin Dan Adam Gaza

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jami'an tsaron Isra'ila sun hallaka Falasdinawa 17

media
Dubban Falasdinawan da ke zanga-zanga a kan iyakar Isra'ila da zirin Gaza. Reuters

Akalla Falasdinawa 17 sun hallaka wasu sama da 1,400 kuma suka jikkata, sakamakon arrangama da sojin Isra’ila, yayin gudanar da zanga-zangar da suka fara jiya a yankin Zirin Gaza.


Falasdinawa 30,000 suka shiga zanga-zangar adawa da hare-haren da sojin Isra’ila ke kaiwa akan yankunansu.

Karo na farko kenan tun bayan rikicin shekarar 2014 da irin wannan arrangama ta auku tsakanin Falasdinawan da sojin Isra’ila, wadanda suka rika amfani da harsasan Roba da na gaske, da kuma hayaki mai sa hawaye, don kokarin tarwatsa zanga-zangar.

Kasar Kuwaiti ta bukaci kwamitin tsaro na majalisari dinkin duniya ya tsawatarwa Isra’ila dangane da yadda take amfani da karfi fiye da kima akan fararen hular na Falasdinawa, bukatar da kwamitin tsaron ya fara nazari akai.

Akwai dai fargabar cewa, yanayin arrangamar tsakanin Falasdinawan da jami’an tsaron Isra’ila ka iya yin muni a kwanaki masu zuwa.