Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

MDD ta hukunta masu fasakaurin mai zuwa Korea ta Arewa

Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya kakaba takunkumai kan wasu kamfanonin sufurin jiragen ruwa hadi da wasu manyan jiragen sakamakon samunsu da laifin fasa kaurin manfetur da makamashin kwal zuwa kasar Korea Ta Arewa.

Zauren Kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya.
Zauren Kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya. Reuters
Talla

Sabbin takunkuman dai sun shafi kamfanonin sufurin jiragen ruwa 21, ciki har da wasu 5 da ke China, sai kuma jiragen ruwa 15 na Korea ta Arewan da wasu 12 da ban a kasar ba.

Matakin kwamitin tsaron yazo ne bayanda shugaban Korea ta arewa Kim Joung Un ya gana da shugaban China Xi Jin Ping, wanda kuma a ranar 27 ga watan Afrilu zai gana da takwaransa na Korea ta Kudu Moon Jae-in, duk akan shirin jingine shirin Korea ta Kudu na ci gaba da kera makaman nukiliya.

A cikin watan Mayu kuma ake sa ran shugaban na Korea ta Arewa zai gana da takwaransa na Amurka Donald Trump.

Sai dai a wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter, Donald Trump ya ce takunkuman da Amurka ta jagoranci kakabawa Korea ta Arewa saboda shirinta na mallakar makaman nukiliya zasu ci gaba da aiki, duk da ganawar da shugabannin kasashen biyu zasu yi nan da gajeren lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.