Isa ga babban shafi
Syria

An cimma yarjejeniyar kwashe marasa lafiya daga birnin Douma

An cimma yarjejeniyar kwashe wadanda suka jikkata daga birnin Douma, gari na karshe a yankin gabashin Ghouta da ya rage a hannun ‘yan tawayen Syria, inda a yanzu za'a tafi da su zuwa birnin Idlib.

Daya daga cikin sassan birnin Douma da hare-haren jiragen yaki suka rusa a Syria.
Daya daga cikin sassan birnin Douma da hare-haren jiragen yaki suka rusa a Syria. REUTERS/Bassam Khabieh
Talla

An cimma yarjejeniyar ce, biyo bayan tattaunawar da aka yi tsakanin mayakan ‘yan tawayen Jaish al-Islam da Rasha.

Har yanzu kuma ‘yan tawayen na ci gaba da tattaunawa da Rasha domin cimma sulhu don dakatar da shirin kaddamar da farmaki kansu da sojin Syria da sukai musu kawanya ke gaf da yi.

Sai dai ‘yan tawayen sun musunta cewa, suna tattaunawa ne da bangaren gwamnati domin kwashe ilahirin dubban fararen hular da ke birnin na Douma.

Bayan shafe makwanni 6 jiragen yakin Syria da hadin gwiwar Rasha suna luguden wuta a gabashin Ghouta, dubban mayakan ‘yan tawaye sun janye daga yankin zuwa arewacin birnin Idlib, a karkashin wata yarjejeniya da suka cimma da sojin gwamnati Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.