rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Falasdinawa Isra'ila Hamas

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Isra'ila ta yi barazanar kaiwa Hamas hare-hare a Zirin Gaza

media
Falasdinawa yayin da suke kwashe wadanda suka jikkata, yayin zanga-zanaga akan iyakar Isra'ila da zirin gaza. REUTERS/Ibraheem Abu Mustafa

Rundunar sojin Isra’ila ta yi gargadin zata iya kai farmaki akan wasu yankunan da ke cikin zirin Gaza, wadanda ta ce ‘yan ta’adda sun yi kakagida a wuraren.


Daya daga cikin manyan jami’an sojin Isra’ila Birgediya Janar Manelis ya shaidawa manema labarai cewa kungiyar Hamas da yankin Zirin Gaza, ta fake ne da zanga-zangar Falasdinawa da ke gudana wajen kai hare-hare cikin Isra’ila.

Gargadin na Isra’ila ya zo jim kadan bayanda Falasdinawa suka yi jana’izar ‘yan uwansu 16 da sojin Isra’ila suka hallaka yayin arrangama da jami’an tsaron, a lokacin zanga-zangar da suka fara tun a ranar Juma’a akan iyakar Isra’ila da Zirin Gaza.

A halin yanzu yawan Falasdinawan da suka jikkata yayin zanga-zangar ya karu zuwa 70.

Dubban Falasdinawa ne ke zanga-zangar neman tilas Isra’ila ta kyale falasdinawa su koma yankunan da a yanzu ta mamaye.