Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falesdinawa

Sojin Israela sun harbe falestinawa 8 har lahira, tare da jikkata 400

Palestinawa takwas sun rasa rayukansu a yayin da wasu 400 suka jikkata sakamakon barin wuta irin na mai kan uwa da wabi da sojojin Israela suka yi kan masu zanga zangar nuna rashin amincewa da killace yankin Gaza da Isarela ta ke yi a wani guri dake kan iyakar da ya raba yankunan 2 a zirin Gaza, mako guda bayan faruwar makamanciyar irin wannan taho mugamar da ta yi sanadiyar mutuwar Palestinawa 17 a yayin da wasu dubu daya suka jikkata sakamakon harin sojojin Isarela akan su.

Falestinawa masu zanga zanga a Gaza
Falestinawa masu zanga zanga a Gaza REUTERS/Ibraheem Abu Mustafa
Talla

A ranar 30 ga watan Maris din da ya gabata farkon barkewar zanga zangar neman komawar yan gudun hijirar palastinawa a gidajensu tare da kawo karshen killace yankin Gazar da Izarelar ta yi, kawo yanzu tashe tashen hankullan sun yi sanadiyar mutuwar palestinawa 19, a ya yinda wasu 1.400 suka jikkata, a taho mugamar da ta kasance mafi muni tun bayan ta shekarar 2014. tsakanin kungiyar Palestinawa ta Hamas da dakarun kasar Isarela.

A yau juma’a dubban palestinawan ne suka sake haduwa a kusa da ganuwar tsaron da ta raba yankin da Israela ta shatawa kanta da na palastinawan da ta killace, a Gaza dake karkashin ikon kungiyar islama ta Hamas, babbar makiyar Isarela.

An samu barkewar tashe tashen hankulla ne a bangarori daban daban da kan ikar da Israelar ta shata ganuwar tsaronta.

Wakilin Afp dake halarta zanga zangar ya ce masu zanga zangar sun ta ciccinawa tayoyin mota wuta, domin hana sojan na Isarela ganin abinda ke faruwa a baya, a yayin da su kuma su kuma suka mayar da martini ta hanyar harbin bindiga da harsasan karfe, inda suka kashe palaestinawa 8, tare da jikkata wasu sama da 400.

Daga cikin wadanda harbin ya jikkata sun hada da maneman labarai guda 6, kamar yadda kungiyar yan jaridun ta sanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.