rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Korea ta Kudu Korea ta Arewa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugabannin kasashen Korea 2 sun buda layukan sadarwa a tsakaninsu

media
Shugaban kasar Korea ta Arewa ©Yonhap via REUTERS

Kasashen Korea ta Arewa da ta Kudu sun bude layukan sadarwa a tsakanin shugabanninsu Kim Jong Un da Moon Jae-in a karon farko a wani mataki na yayyafawa zukatansu ruwa bayan tankiyar da ta dade a tsakaninsu.


Layukan dai za su kasance masu sadar da fadar shugaban kasa ta Blue House da ke a birnin Seoul na kasar Korea ta kudu, da kuma Ofishin kula da harkokin gwamnatin kasar Korea ta Arewa inda shugaba Kim ke jagorantar wani bangare na gwamnatinsa.

Yanzu haka dai an bude wannan hadin layuka tsakanin shugabannin guda biyu inda akasamu kyakkyawan hanyar sadarwa da batada matsala a tsakaninsu.

Ko a taswirar kassahe ma kasashen Korea ta Kudu da ta Arewa na zaman tamkar Kofa da Kofa ne amma aka raba kasashen akalla shekaru 70 da sukja gabata, ba tare da samun ko sadarwa daya a tsakanin al’ummar kasashen biyu ba, tun bayan yakin da aka gwabza a shekarar 1953.