rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Korea ta Arewa Korea ta Kudu Amurka China

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasashen Duniya sun yi na’am da jingine Nukiliyar Korea ta Arewa

media
Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un 路透社

Shugabannin kasashen Duniya sun fara maida martani mai dadi dangane da alkawarin da shugaban kasar Korea ta Arewa ya dauka na cewar daga yanzu ya daina gwajin makamin Nukiliya.


To sai dai shugaba Kim bai fayyace ko kasar tasa na shirin dakatar da kera makaman Nukiliyar ko a'a ba, amma duk da haka, sa’o’i kalilan da ya bayyana daukar wannan mataki, shugaban kasar Amurka Donald Trum ya bayyana matakin a matsayin babban ci gaba da suka yi jira.

Sakataren Majalisar dinkin Duniya Antonio Guterres ya yaba wa shugaban kasar ta Korea ta Arewa akan diyaucin da ya nuna.

Kasashen Japan da China duka na masu na’am da wannan matakin da shugaba Kim ya dauka, a yayinda kungiyar tarayyar Turai ke maraba da jin wannan maganar.

Kasar Rasha ma na mai bayyana hakan a matsayin babban abin ci gaba da hakan ke iya kawowa ga samar da zaman lafiya a Duniya.

Kasar Amurka dai na bukatar kasar Korea ta Arewa da jingine aikin sarrafa sinadaran da ke samar da makamin Nukiliya da ma daina kera makaman na Nukiliyar ne tun a shekarun baya, a yayin da Korea ta Arewan ke bayyana aikin samar da Nukiliyar a matsayin matakin kariyar kai daga barazanar wasu kasashen Duniya.

A baya dai kasar ta Korea ta Arewa ta sha nunawa Duniya cewar tana da makaman na Nukiliya tare da yin gwajinsu ba tare da masaniyar hukumar kula da makaman kare-dangi ta majalisar dinkin Duniya ba.