rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Falasdinawa Isra'ila Gaza Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sojin Isra'ila sun hallaka Falasdinawa 44 a Gaza

media
Dubban Falasdinawa da ke zanga-zanga a kan iyakar Isra'ila da zirin gaza. Reuters/Mohammed Salem

Jami’an tsaron Isra’ila sun harbe wasu karin Falasdinawa uku har lahira, yayin da dubban Falasdinawan suke ci gaba da zanga-zanga akan iyakar Isra’ila da Gaza, cikin mako na biyar a jere.


Ma’aikatar lafiya ta yankin na Gaza ta ce sama da Falasdinawa 300 yanzu haka ke karbar magani, sakamakon samun raunukan harbin bindiga.

Zuwa yanzu dai jami’an tsaron Isra’ila sun hallaka Falasdinawa 44 tare da jikkata wasu kimanin 1,500, tun bayan fara zanga-zangar da suka yi a ranar 30 ga watan Maris.

Falasdinawan na zanag-zangar ce don tilastawa gwamnatin Isra’ila basu damar komawa yankunansu da ta kwace a shekarar 1948.