rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Korea ta Arewa Korea ta Kudu Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Korea ta Arewa zata rufe cibiyar gwajin nukiliyarta a watan Mayu

media
Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong-un da takwaransa na Korea ta Kudu Moon Jea-in yayin tattaunawa mai cike da tarihi a ranar 27, Afrilu 2018. 路透社。

Korea ta Kudu ta ce a watan Mayu mai kamawa Korea ta Arewa zata rufe cibiyar da take amfani da ita wajen gwajin makaman nukiliya.


Kakakin shugaban kasar Korea ta Kudu, Yoon Youn-chan, ya ce za’a yi bikin rufin cibiyar ta Punggye-ri ce a bainar jama’a, bisa sa’idon jami’anta da kuma tawaga daga kasar Amurka.

Sau shidda Korea ta Arewa tana gudanar da gwajin nukiliya a cibiyar ta Punggye-ri tun daga shekarar 2006.

Gwaji na karshe da aka yi a cibiyar ya gudana ne a cikin watan Satumba na 2017, wadda ya haddasa motsawar kasa a yankin.

A ranar Juma’ar da ta gabata, yayin ganawar da suka yi, shugaban Korea ta Arewa Kim Jong-un da takwaransa na Korea ta Kudu Moon Jea-in, suka amince da kawo karshen duk wani shirin mallakar makaman nukiliya a baki dayan yankin na Korea.