rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Gabas ta Tsakiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sakataren harkokin wajen Amurka na ziyara a Gabas ta Tsakiya

media
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo yayin gaisawa da Fira Ministan harkokin waje na Saudiya Adel Al-Jubeir a birnin Riyadh. Reuters

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya isa kasar Saudiyya, inda ya fara ziyarar kwanaki uku a yankin gabas ta tsakiya, wadda a cikinta zai ziyarci kasashen Jordan da Isra’ila.


Ana sa ran ziyarar ta Mike Pompeo zata mayarda da hankali ne akan yarjejeniyar nukuliyar Iran, wadda shugaban Amurka Donald Trump ke fatan a yiwa garambawul.

A farkon shekarar da muke ciki ne kuma Trump ya yi barazanar janye amurka daga yarejejeniyar, muddin ba a sauya mata fasali ba, nan da zuwa 12 ga watan Mayu.

Kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar nukiliyar Iran a shekarar 2015, sun hada da Birtaniya, Faransa, Jamus, Rasha da kuma China.

Ra’ayin baki dayan kasashen ya ci karo da na Amurka da ke neman a sake fasalta yarjejeniyar, kudurin da itama kasar Iran da ci alwashin ba zata lamunci kyale aiwatar da shi ba.