Isa ga babban shafi
Afghanistan

Hare-haren bam sun hallaka mutane 36 a Afghanistan

Akalla mutane 25 ne suka hallaka a wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake da aka kai a Kabul, babban birnin Afghanistan.

Kungiyar IS ta yi ikirarin kai hare-haren birnin Kabul.
Kungiyar IS ta yi ikirarin kai hare-haren birnin Kabul. REUTERS
Talla

Babban wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa AFP mai daukar hoto a Kabul, Shah Marai, na daga cikin wadanda suka hallaka.

Bam na farko ya tashi ne a lokacin da mahari na farko bisa kan babur ya tarwatsa shi, yayinda bam na biyu ya tarwatse, bayanda jama’a suka dandazo a wurin don baiwa idanunsu abinci, ciki harda manema labarai.

Ma’aikatar harkokin cikin gidan Afghanistan ta ce yawan wadan suka jikkata ya kai 49.

Tuni dai kungiyar IS ta dauki alhakin kai hare-haren.

Har ila yau akalla kananan yara 11 ne suka hallaka, a wani harin da kungiyar ta IS ta yi ikirarin kaiwa kan sojojin kungiyar kawancen tsaro ta NATO a lardin Kandahar.

A farkon watan Afrilu, wani harin kunar bakin waken da aka kai a wata cibiyar yiwa masu kada kuri’a rijista birnin Kabul, yayi sanadin hallakar mutane 60, tare da raunata wasu 119.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.