rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Myanmar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dole a tsananta bincike kan zargin cin zarafin 'yan Rohingya- MDD

media
Wasu tarin musulmai 'yan kabilar Rohingya kenan lokacin da wasu jami'an tsaro ke azabtar da su a kauyen Inn Din na jihar Rakine. 路透社。

Wakilan Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ke rangadi tare da bin diddigin zargin cin zarafin musulmi 'yan kabilar Rohingya a Myanmar sun bukaci gudanar da wani kwakkwaran bincike don gano gaskiyar zargin da ake na cewa jami'an kasar ta Myanmar sun ci zarafin tsirarun 'yan kabilar ta Rohingya musulmi.


Karen Pierce wadda jakadar Birtaniya ce a Majalisar Dinkin Duniya ta fadawa manema labarai bayan da ta ziyarci matsugunan da musulmin Rohingyar ke gudun hijira a Bangladesh da kuma Jihar Rakhine a Myanmar cewa dole ne a tsananta bincike kan zarge-zargen.

Musulmi 'yan kabilar Rohingya dai na zargin hukumomi a Myanmar da cin zarafinsu, musamman ta hanyar amfani da jami'an soji matakin da ya tilasta musu kauracewa muhallansu don tsira da rayukansu.

Kafin yanzu dai bangarori da dama ne suka yi ta kiraye-kirayen ganin an dauka tsauraran matakai kan cin zarafin 'yan kabilar ta Rohingya musamman ganin yadda suka nuna tirjiya kan batun komawarsu gida.