Isa ga babban shafi
India

Guguwa mai dauke da rairayi ta hallaka mutane 95 a India

Wata mahaukaciyar guguwa da ta ratsa yankin arewacin India, ta hallaka akalla mutane 95, tare da jikkata wasu 143, yayinda kuma guguwar ta tumbuke bishiyoyi da kuma rusa gine-gine masu yawan gaske.

Wasu Indiyawa mata a gabar kogin Ganges a garin Allahabad na kasar India yayinda suke kokarin gujewa guguwa mai dauke da yashi da at ratsa ta yankin.
Wasu Indiyawa mata a gabar kogin Ganges a garin Allahabad na kasar India yayinda suke kokarin gujewa guguwa mai dauke da yashi da at ratsa ta yankin. Reuters
Talla

Jami’an agaji sun ce guguwar ta ratsa ne ta jihohin Uttar Pradesh da Rajasthan, kuma akwai yiwuwar a samu Karin yawan wadanda suka rasa rayukansu.

Mutane 64 ne suka hallaka a Uttar Pradesh kadai, yayinda wasu 31 suka hallaka a jihar Rajasthan.

Jami’ai sun ce mafi akasarin wadanda suka mutu ku suka jikkata gine-gine da bishiyoyi ne suka auka musu, yayinda suke tsaka da barci.

Tuni dai gwamnatin kasar ta sanar da cewa zata baiwa iyalan wadanda suka rasa rayukansu Rupee 400,000 a matsayin diyya.

Guguwar ta kuma afkawa Delhi, babban birnin kasar ta India cikin gudun sama da kilomita 100 dauke da ruwan sama mai karfin gaske.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.