Isa ga babban shafi
Asiya

Kasashen Asiya 4 sun kulla yarjejeniyar hana yaduwar makamai

Kasashen China da Japan da Korea ta kudu, sun amince da yarjejeniyar hana yaduwar makaman kare dangi a yankin Korea. Firamnistan kasar Japan Shinzo Abe ya ce a yaunzu nauyi ne da ya rataya ga kasar Korea ta Arewa ta sa Ido sosai akan wannan aikin da za a gudanar.

Har Ila yau akwai jayayyar da ke tsakanin kasashen biyu akan yankunan kan iyakokinsu musamman Senkakus a Japan da kuma Diaoyu a China.
Har Ila yau akwai jayayyar da ke tsakanin kasashen biyu akan yankunan kan iyakokinsu musamman Senkakus a Japan da kuma Diaoyu a China. REUTERS/Toru Hanai
Talla

Kasar Korea ta Arewa wadda ta yi ayyukan samarwa kanta makaman Nukiliya ta hanyar kin bada kai ga hukumar tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya, ta samu matsayi na yin ruwa-tsaki a tattaunawar da shugabannin kasashen 3 za su gudanar a birnin Tokyon kasar Japan, bayan wani taro da aka gudanar tsakanin shugabannin kasashen Korea ta Kudu da Arewa.

An ce dai Kim na shirin tattaunawa da shugaba Donald Trump na Amurka bayan kammala taron na su, kuma kasashen 3 duka sun amince su hada kansu musamman lura da jituwar baya-bayan nan da aka sama a tsakanin Korea ta Kudu da ta Arewa.

To sai dai har yanzu ana ganin kasashen na Korea ta Arewa da Kudu na zaman Doya da Manja ne kawai, saboda zaman lafiyar da ke tsakaninsu na yarjejeniya ne ba na din din din ba.

Duk da su kansu kasashen China da Japan masu zaman na 2 da na 3 a karfin tattalin arziki a Duniya, na cikin wata takaddama ne ta tsamin dangantaka mai nasaba da albarkatun karkashin Teku.

Har Ila yau akwai jayayyar da ke tsakanin kasashen biyu akan yankunan kan iyakokinsu musamman Senkakus a Japan da kuma Diaoyu a China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.