rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Malaysia

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Firaminista mafi yawan shekaru a duniya zai sha rantsuwa a yau

media
Zabebben Firaministan Malaysia Mahathir Mohamad mai shekaru 92 da haihuwa REUTERS/Lai Seng Sin

Tsohon shugaban Malaysia Mahathir Mohamad mai shekaru 92 da haihuwa ya shirya karbar rantsuwar kama aiki a wannan Alhamis bayan zaben sa a matsayin sabon Firaminista mafi yawan shekaru a duniya.


Mahathir da ya tsaya takara a karkashin hadakar jam’iyyun adawa na kasar, ya samu gagarumin rinjaye a fafatawarsa da abokin takararsa na jam’iyyar Barisan Nasional da ta fara mulkin kasar tun bayan samun ‘yanci a shekarar 1957.

Mahathir da ya taba mulkin kama-karya na tsawon shekaru 22 a Malaysia, ya doke Firaminista mai ci Najib Razak sakamakon zarge-zargen cin hanci da rashawa da suka kanannade shi.

Sabon Firaministan ya janye daga ritayarsa kafin daga bisani ya sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa don fafatawa da jam’iyya mai mulkin kasar.

Tuni magoya bayansa suka fantsama kan tituna don nuna murnar nasarar da ya samu a zaben.

Ana sa ran rantsar da sabon Firaministan da misalin karfe 5 na yamma a gogon Malaysia, wanda ya yi dai dai da karfe 9 agogon GMT.