rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Indonesia ISIL Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan kunar bakin wake sun kai hari kan mujami'u a Indonesia

media
'Yan sanda kasar Indonesia a harabar daya daga cikin mujami'un da 'yan kunar bakin wake suka kaiwa hari a Surabaya. Antara Foto/M Risyal Hidayat /REUTERS

‘Yan sandan Indonesia sun ce wasu ‘yan kunar bakin wake sun hallaka mutane 11 a Surabaya, birni na biyu mafi girma a kasar.


‘Yan Kunar bakin waken sun kai hari ne kan wasu mujami’u 3 da ke birnin na Surabaya, inda suka jikkata mutane 40.

Kakakin hukumar binciken sirri na kasar ta Indonesia Jemaah Ansharut Daulah ya ce akwai kyautata zaton kungiyar IS ce ta shirya kai harin.

Harin shi ne mafi muni, tun bayan wanda wasu 'yan kunar bakin wake suka kai a tsibirin Bali cikin shekarar 2005, inda suka hallaka mutane 20.

Zalika hukumomin tsaron kasar sun ce hare-haren suna da nasaba, da gumurzun da akai da wasu mayakan kungiyar ta IS, da sukai yunkurin tserewa daga wani gidan yari a gaf da babban birnin kasar Jakarta, bayanda suka hallaka jami’an tsaro biyar.