rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

India

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Zabtarewar laka sakamakon kakkarfan ruwan sama a India

media
Wasu yankuna kasar India da aka samu ambaliya REUTERS/Danish Siddiqui

Wani sabon ibtila’in zabtarewar laka sakamakon kakkarfan ruwan sama hade da iska a India ya hallaka akalla mutane 40 a yau lahadi.


Iskar mai karfin gaske wadda ke gudun kilomita 100 a cikin sa a guda ya haddasa kakkaryewar turakun lantarki tare da balle tekuna, matakin da ya haddasa ambaliyar ruwa tare da zabtarewar laka.

Kawo yanzu dai lamarin ya shafi yankuna da dama da suka hadar da Utter Pradesh da Bengal da Andhra da kuma wasu sassa na New Delhi babban birnin kasar India.