rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Malaysia

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gwamnatin Malaysia ta yiwa Anwar Ibrahim afuwa

media
Anwar Ibrahim tsohon Firaministan kasar Malaysia REUTERS/Bazuki

Hukumomin Kasar Malaysia sun saki tsohon Firaminista Anwar Ibrahim daga gidan yari, bayan afuwar da aka masa, matakin da zai bashi damar komawa fagen siyasa.


Anwar ya bar asibitin Kuala Lumpur da aka masa aiki a kafadar sa yana murmushi da kuma daga hannu ga tarin yan Jaridun da suka mamaye kofar shiga asibitin kafin ya shige motar sa ba tare da ya yi jawabi.

Sabon Firaminista Mahathir Muhammed ya sanar da afuwar da aka masa wanda yake daya daga cikin yarjejeniyar da ya kulla da jam’iyyun kawancen da suka bashi damar samun nasarar zabe.