rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Malaysia

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yan Sanda sun gudanar da bincike a gidan Najib Razak

media
Najib Razak.tsohon Firaministan kasar Malaysia Reuters

‘Yan sandan Malaysia sun kai samame kan wasu gidajen tsohon Firaministan kasar Najib Razak a Kuala Lumpur, inda suka shafe sa’oi suna gudanar da bincike akan zarge zargen karkatar da kudade da ake zarginsa da yi.


A makon da ya gabata ne sabon Firaministan kasar Mahathir Muhd ya haramtawa Najib da mai dakinsa tafiya zuwa ketare har sai abinda hali yayi a binciken da yake gudana a kansa, zarge-zargen da tsohon Firaministan ya sha musantawa.

Kungiyoyin kare hakokin bil adam a kasar na bukatar gani an kare lafiyar tsohon Firaministan da mai dakinsa tareda baiwa alkalai damar gudanar da ayyukan bisa gaskiya.