rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Saudiya Habasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Saudiya ta saki fursunoni 1000 'yan kasar Habasha

media
Wasu daga cikin bakin-haure 'yan kasar Habasha da Saudiya ta maida gida. Reuters

Gwamnatin Saudiya ta amince da sakin fursunoni ‘yan kasar Habasha 1,000 da take tsare da su, wadanda ta kama bisa aikata laifuka daban daban ciki har da mata dari.


Matakin ya biyo bayan rokon da Fira Ministan Habasha, Abiy Ahmed ya yi, wanda yake ziyara a kasar.

A halin da ake ciki hukumomin Saudiya na kan aiwatar da shirin maida ‘yan kasar ta Habasha kimanin 500,000 gida, wadanda ke zaune a kasar ba bisa ka’ida ba, kuma zuwa yanzu an mayar da bakin hauren 160,000.

Akwai dai dubban daruruwan ‘yan kasar Habasha da ke zama a yankin gabas ta tsakiya, mafi akasarinsu kuma suna zaune ne a Saudiya.