Falasdinawa Isra'ila Gaza Hakkin Dan Adam
wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa
Isra’ila zata gina karin gidaje 1,958 a Zirin Gaza

Wata kungiya mai kula da matsugunnan yahudawa ta ce Isra’ila ta amince da gina karin muhallan yahudawa ‘yan kama-wuri-zauna 1,958 a wani sabon wuri da ke a yankin zirin Gaza.
Adadin sabbin matsugunnan da hukumomi a kasar Isra’ila suka amince da ginawa, wasu ne daga cikin adadin 2,500 da ministan tsaron kasar ya gabatarwa majalisar zartaswar kasar.
Amincewa da sake gina sabbin gidajen shi ne na farko tun bayan da kasar Amurka ta maida Ofishin jekadancinta zuwa birnin Kudus a ranar 14 ga watan Mayu na wannan shekara, matakin da ya haddasa bore da ya kai ga dakarun Isra’ila suka hallaka Falasdinawa sama da 60 a wuni daya.
Zuwa yanzu akalla Yahudawa 500,000 ne suka zaune a yankunan da Isra’ila ta kwace daga Falasdinawa a yankunan Yamma da kogin Jordan da kuma gabashin Birnin Kudus.