Isa ga babban shafi
Iraqi

An yanke wa wata mata ‘yar Faransa hukuncin kaso a Iraqi

Wata Kotu a kasar Iraqi ta yanke wa wata mata 'yar kasar Faransa hukuncin zama gidan yari har iyakar rayuwarta, wannan kuwa na da nasa ba ne da samunta da laifin shiga kungiyar IS

Melina Boughedir wata bafaranshiya da aka kama da laifin zama yar kungiyar IS a Iraqi
Melina Boughedir wata bafaranshiya da aka kama da laifin zama yar kungiyar IS a Iraqi Stringer/AFP
Talla

Kotu a kasar Iraqi ta yanke wa wata mata mai suna Melina Boughedir hukuncin daurin shekarun 20, saboda samun ta da laifin alaka da kungiyar yan ta'adda ta IS.

A watan Fabarairun da ya gabata ma an yanke wa Melina Boughedir mai ‘yaya hudu, hukuncin daurin watanni 7 saboda samun ta da laifin shiga Iraki ba a kan ka’ida ba, kuma a yayin da ake kokarin taso keyarta zuwa Faransa ne aka gano cewa tana da alaka da kungiyar ta IS.

Hukumomi a kasar Iraqi dai sun kama yan kasashen waje da dama da hannu dumu-dumi a cikin kungiyar ta IS mai ikirarin kaddamar da yakin jahadi a kasar ta Iraqi.

A ranar Lahadin da ta gabata ne bincike ya kama Melina da hannu tsamo-tsamo a cikin kungiyar ta IS aka kuma yanke mata hukuncin daurin rai-da-rai. To sai dai Melina ta sha bayyana wa cewar ita bata da laifi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.