rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Saudiya Yemen

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Harin makami mai linzami ya hallaka fararen hula a Saudiya

media
Wani makamin Saudiya a kan iyakarta da Yemen, yayin da ta harba shi kan 'yan tawayen Houthi, ranar 15 ga watan Afrilu, 2015. Reuters

Saudiya ta ce fararen hula uku sun hallaka a garin Jizan da ke kudancin kasar, a wani harin makamai mai linzami da ake kyautata zaton cewa ‘yan tawayen Houthi na kasar Yemen suka kai.


Kakakin rundunar sojin Saudiya, Kanal Turki al-Maliki ya ce da gangan mayakan na Houthi suka kai harion kan fararen hular a daren jiya Asabar.

A yan watannin baya bayan nan dai, mayakan na Houthi sun harba makamai masu linzami cikin Saudiya a lokuta daban daban, inda wasu suka fada babban birnin kasar Riyadh.

A watan Maris na shekarar 2015, Saudiya ta kaddamar da yaki kan ‘yan tawayen na Houthi, bayan da suka hambarar da gwamnatin waccan lokaci da ke birnin Sana’a.

Yakin da bangarorin biyu ke ci gaba da gwabzawa ya haddasa hasarar sama da rayukan fararen hula 10,000 a kasar Yemen, yayinda kuma ya haddasa bala'in yunwa da barkewar cutuka a yankunan kasar, biyo bayan rufe kan iyakokin Yemen din da kowane bangare ya yi, inda yake da karfin iko.