rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Isra'ila Falasdinawa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasashe 120 sun yi Allah wadai da Isra'ila

media
Wasu daga cikin dubban Falasdinawa da ke zanga-zanga a kan iyakar Isra'ila da zirin gaza. AFP Photo/MAHMUD HAMS

Kasashe 120 sun kada kuri’ar yin tir da kuma Allah wadai da hare-haren da Isra’ila ke kai wa tare da hallaka Falasdinawa 129 yankin Gaza.


Zauren majalisar dinkin duniya mai manbobi 193 ya kuma yi watsi da yunkurin Amurka na dora laifin tashin sabon rikicin da a yanzu ya shafe sama da watanni 2, akan kungiyar Hamas.

A ranar 30 ga watan Maris Falasdinawa suka kaddamar da wata zanga-zangar cika shekaru 70 da zagayowar ranar da Isra’ila da kori kimanin Falasdinawan dubu 750 daga gidajensu.