rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Yemen

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ana ci gaba da gwabza fada a Hodeida na kasar Yemen

media
Tashar jiragen ruwa a kasar Yemen DR

A rana ta biyu da dakarun kawancen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya suka kaddamar da farmaki domin sake kwato garin Hodeida mai tashar jiraren ruwa daga ‘yan tawayen Huthi, rahotanni sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 39 mafi yawansu fararen hula a jiya alhamis.


A jiya alhamis kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da zama na musamman a asirce dangane da rikicin na Yemen, inda kasashe suka bayyana fargabarsu dangane da yiyuwar samun cikas a ayyukan jinkai ga milyoyin mutanen kasar, lura da cewa mafi yawan kayayyakin agaji ana shigar da su ne daga tashar ruwan garin na Hodeida.