rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Afghanistan Taliban

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Taliban ta yi watsi da tayin kara wa'adin tsagaita wuta

media
Wani mayakin kungiyar Taliban tsaye a bangaren dama, yayin da jami'an tsaron Afghanistan ke sintiri a cikin motar soji, yayin bikin ranar Sallah, a lardin Nangarhar. REUTERS/Parwiz

Kungiyar Taliban ta yi watsi da tayin kara wa’adin yarjejeniyar tsagaita wutar da ta sanar tsakaninta da dakarun Afghanistan, domin bai wa ‘yan kasar damar hutun Salla cikin kwanciyar hankali.


Cikin sanarwar da ta fitar, kungiyar ta ce, yarjejeniyar da ta ke kai , za ta kare ne a daren yau Lahadi, kuma kai tsaye za ta ci gaba da kai wa sojin gwamnati hare-hare.

A ranar Asabar, shugaban Afghanistan Ashraf Gani ya roki kungiyar ta Taliban, ta bi sawun matakin da ya dauka na tsawaita wa’adin yarjejeniyar tsagaita wutar da suka sanar gabannin ranar Salla, abinda ya baiwa mayakan damar shiga cikin biranen kasar tare da gaisawa cikin raha da sojin kasar da fararen hula cikin raha.

A gefe guda yayin da yarjejeniyar tsagaita wutar ke ci gaba da aiki a ranar Asabar, wani harin kunar bakin wake da aka kai kan wani taron mayakan Taliban da jami’an gwamnati, ya hallaka mutane 36 a lardin Nangarhar, wanda kungiyar IS ta yi kirarin kai wa.