rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Afghanistan Taliban

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Masu tattaki a Afghanistan don samar da zaman lafiya sun isa Kabul

media
Tattakin masu fafutukar ya fara ne tun kafin watan Ramadana inda su ke da fatan ganin an samu jituwa tsakanin gwamnati da kungiyar Taliban don samar da wanzajjen zaman lafiya a kasar ta Afghanistan da ke fuskantar yake-yake. REUTERS/Mohammad Ismail

Masu fafutukar samar da zaman lafiya a kasar Afghanistan wadanda suka yi tattaki na tsawon kilomita 700 a cikin kwanaki 40, a yau litinin sun isa Kabul fadar gwamnatin kasar.


Masu tattakin sun zagaya a biranen kasar da dama a kafa a duk tsawon watan Ramadana, inda suke yi kira ga gwmanatin da kuma ‘yan Taliban da su rungumi zaman lafiya.

Sai dai kuma Isar masu faftukar birnin Kabul na zuwa a dai dai lokacin da Taliban ta yi watsi da tayin kara wa'adin tsagaita wuta tsakaninsu da Sojin kasar da kuma na hadaka.

Tun farko dai gwamnatin ce ta bukaci tsagaita wutar don gudanar da bukukuwan sallah Lafiya inda kuma daga bisani ta bukaci tsawaita wa'adin amma Taliban ta  ki.

Fatan masu faftukar bai wuce ganin an kawo karshen rikicin da ke tsakanin bangarorin biyu ba, tare da ganin an samu wanzuwar zaman lafiya a kasar.