rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Yemen Saudiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yemen: Mutane 5,000 sun rasa muhallansu a Hodeida

media
Daya daga cikin motocin mayakan Houthi da hare-haren dakarun Saudiya suka lalata, a yankin al-Fazah da ke lardin Hodeida a kasar Yemen. AFP

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla iyalai 5000, sun rasa muhallansu a Yemen, sakamakon hare-haren da dakarun kawance na Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya suka kaddamar, don kwace birnin Hodeida mai tashar jiraren ruwa daga ‘yan tawayen Houthi.


A ranar Larabar makon jiya ne, rundunar dakarun kawancen Larabawan karkashin Saudiyya ta kaddamar da sabbin hare-haren.

Majalisar dinkin duniya ta ce tun daga ranar 1 ga watan Yuni kimanin iyalai 4, 458 suka rasa matsugunansu, yayinda hare-haren ya lalata musu gidaje da gonaki.

Majalisar ta kara da cewa yanzu haka akwai fiye da mutanen miliyan 22 a kasar ta Yemen da ke bukatar agajin gaggawa ciki har da wasu miliyan 8 da rabi, da ke cikin hadarin fuskantar tsananin Yunwa.

A alhamis din da ta gabata ne kwamitin tsaron MDD ya gudanar da zama na musamman a asirce kan rikicin na Yemen, inda kasashe suka bayyana fargabarsu dangane da yiwuwar samun cikas a ayyukan jinkai ga milyoyin mutanen kasar, lura da cewa mafi yawan kayayyakin agaji ana shigar da su ne daga tashar ruwan garin na Hodeida.