rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iraqi Syria ISIL

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sojin Iraqi sun hallaka mayakan IS 45

media
Sojin Iraqi sun hallaka kwamandojin IS a Syria. REUTERS/Omar Sanadiki

Rundunar sojin Iraqi ta ce ta yi nasarar hallaka mayakan kungiyar IS 45, ciki harda manyan kwamandojinsu, a wani farmaki da ta kai kan wata maboyarsu da ke garin Hajin a gabashin kasar Syria a lokacin da suke taro.


Karo na biyu kenan da sojin na Iraqi ke kai irin wannan farmaki cikin wata guda.

A watan Mayu da ya gabata ne kungiya mai sa ido kan yakin Syria, wato Syrian observatory, ta bada rahoton cewa akwai mayakan IS akalla 65 da ke zaune a garin na Hajin.

Tun daga shekarar da ta gabata ne sojin Iraqi suka kaddamar da farmaki kan mayakan IS da ke Syria, bayan samun amincewar shugaban kasar Bashar al-Assad da kuma bangaren rundunar mayakan da Amurka ke jagoranta.