rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Saudiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mata sun soma tuka mota a Saudiya

media
Mata sun soma tuka mota a Saudiya REUTERS/Faisal Al Nasser

A yau lahadi ne dokar baiwa mata damar tuka mota ta soma aiki a kasar Saudi Arabia a karon farko.

Kasar ta amince da dokar bai wa mata damar tuka mota, matakin ya kawo karshen haramcin, wanda ya nuna cewar kasar ce kasa daya tilo da ke amfani da irin wannan doka.


Sarki Salman bin Abdulaziz ya bada umurnin cire haramcin a shekara ta 2017,wacce ta soma aiki a yau 24 ga watan yuni shekarar 2018,matakin da zai ba matan damar karbar lasisi da kuma tuka mota kamar takwarorinsu na kasashen duniya.

Dokar ba matan damar tuki ta soma aiki a yau, mahukuntan kasar sun yi tanadin lasisin tukin ga Mata kamar dai yada rahotanni suka nuna.

Kasashen duniya da kungiyoyin kare hakkin Bil Adama sun yaba da wannan mataki wanda a baya suke kallon haramtawa mata tuki a Saudiya a matsayin wani nau’in cin zarafi.