rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Turkiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An soma zaben kasar Turkiya

media
Zaben kasar Turkiya REUTERS/Goran Tomasevic

Hukumar zaben kasar Turkiya ta bayyana cewa mutane milyan 56.3 ne suka samu yi rijista tareda karbar katunan zabe ,wasu milyan uku dake zaune a kasashen waje sun gudanar da na su zaben tun ranaku 7 da 19 ga wannan watan da muke cikin sa.


Ruhunan zabe 181.000 ne aka tabbatar za su bude a yau lahadi a zaben da hada da na yan majalisu .

Yan takara shida da suka hada da Shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan ne za su fafata wajen neman kujerar shugabancin kasar ta Turkiyya da ake sa ran Shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan zai lashe.

Daga cikin alkawuran da yan takara irin su shugaba mai ci Recep Tayyip Erdogan da abokin hamayyarsa, sun sha alwashin komar da milyoyin yan gudun hijira kasar su.

Alwashin 'yan takarar ya biyo bayan cece kucen da masu kada kuri’a ke yi akan adadin 'yan gudun hijira da ke Turkiya.