rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Myanmar Antonio Guterres

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gutteres zai ziyarci 'Yan gudun hijirar Rohingya da ke Bangladesh

media
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. REUTERS/Mike Segar

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteress zai fara wata ziyara zuwa Bangladesh tare da rakiyar shugaban bankin duniya Jim Yong Kim don nazarta bukatar dubban musulmi ‘yan kabilar Rohingya da rikici ya rabo su da Myanmar bayan kisan kiyashin da aka yi musu.


Sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ta ce ziyarar ta kwanaki 2 na a matsayin nuna ban girma ga Bangladesh wadda ta taka rawar gani wajen bayar da matsugunai ga dubban ‘yan gudun hijirar tun daga bara zuwa yanzu.

Tun bayan fara kai musu hare-haren kare dangin cikin watan Agusta akalla musulmi marasa rinjaye ‘yan kabilar Rohingya daga kasar Mynamar fiye da dubu dari 7 ne su ka yi hijira zuwa makociyar kasar Bangladesh don tsira da rayukansu.