rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Japan Muhalli

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ambaliyar ruwa ta raba sama da mutane miliyan 2 da muhallansu

media
Yankin Okayama na kasar Japan, daya daga cikin wuraren da ambaliyar baya bayan nan ta shafa. Kyodo/via REUTERS

Jami’an agaji a Japan sun ce yawan wadanda suka hallaka a kasar sakamakon ambaliyar ruwan da ta aukawa yankunan yammaci da tsakiyar kasar ya karu daga 49 zuwa 60.


Zalika jami’an wadanda suka bayyana fargabar karuwar hasarar rayukan sun ce mutane 73 suka jikkata a Iftila’in, yayinda wasu masu yawan gaske suka bata.

Sama da mutane miliyan biyu ambaliyar ruwan ta tilastawa tsreewa daga muhallansu, bayan da manyan kogunan da suka tumbatsa suka shafi kauyuka da dama.

Ma’aikatar lura da yanayin kasar ta Japan ta yi gargadin cewa ko da ruwan saman zai yi sauki, to fa akwai sauran hadarin da ke fuskantar yankunan da ambaliyar ta shafa la’akari da cewa za a iya samun zaftarewar kasa.