Isa ga babban shafi

Harin kunar baki wake ya hallaka sama da mutane 120 a Pakistan

An samu karuwar wadanda suka hallaka a harin kunar bakin waken da aka kai kan wani gangamin siyasa a garin Mastung da ke kudu maso yammacin Pakistan.

Harabar filin da dan kunar bakin wake ya kai wa masu gangamin siyasa hari a yankin kudu maso yammacin kasar Pakistan.
Harabar filin da dan kunar bakin wake ya kai wa masu gangamin siyasa hari a yankin kudu maso yammacin kasar Pakistan. AFP
Talla

A halin da ake ciki gwamnatin kasar ta yawan wadanda suka hallaka a harin ya haura 100.

Yayin da yake karin bayani halin da ake ciki, Ministan harkokin cikin gidan kasar ta Pakistan Agha Umar Bungalzai ya tabbatar da rahoton jami’an agaji da ke bayyana cewa mutane 128 ne suka hallaka a wannan harin kunar bakin wake, yayin da wasu 150 kuma suka jikkata.

Harin na garin Mastung, dai shi ne mafi muni da aka taba kai wa a kasar ta Pakistan a baya bayan nan, tun bayan kai wani makamancinsa a shekarar 2014.

Harin wanda kungiyar IS ta yi ikirarin kai wa, ya zo ne sa’o’i kalilan bayan da mutane akalla hudu suka hallaka wasu 39 kuma suka jikkata a garin Bannu a arewa maso yammacin kasar ta Pakistan da ke iyaka da Afghanistan.

Har-haren dai sun jefa tsoro a zukatan mafi akasarin ‘yan kasar, ganin cewa a ranar 25 ga watan Yuli mai zuwa ake sa ran gudanar da manyan zabukan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.