rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

China

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wani hadari a China ya haddasa mutuwar mutane 19

media
Yankin Tianjin,daya daga cikin yankunan da aka fi samu hadura a kasar China REUTERS/Stringer

Wasu mutane 19 sun mutu sakamakon wani hadari da aka samu a yankin da ake da masana’antun Sichuan dake kasar ta China.


Rahotanni sun ce an samu hadarin ne a wani kamfani wanda ya haifar da wata fashewa mai karfi kafin hayaki ya tirnike ginin.

Ya zuwa yanzu ba’a san abinda ya haifar da hadarin ba, amma hukumomi sun ce anyi nasarar kashe wutar.

A yan shekaru da suka gabata an sha samu mutuwar mutane sakamakon hadura daga Kamfanoni.

A shekara ta 2015 kusan mutane 165 ne suka mutu a yankin Tianjin dake arewacin kasar sanadiyar wuta a wata masana’antar dake yankin.