rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
  • Palestinawa 22 hare-hare daga Israela ya kashe a Gaza.
  • Dan kunar bakin wake ya kashe mutun daya a ofishin 'yan sandan Indonesia

Korea ta Kudu Rashawa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Park Guen Hye na fuskantar zaman shekaru 32 a yari

media
Park Geun-hye tsohuwar Shugabar kasar Koriya ta kudu REUTERS/Kim Hong-Ji

Wata kotu a kasar Koriya ta Kudu ta sake yankewa tsohuwar shugabar kasar Park Guen Hye hukuncin daurin karin shekaru 8 saboda karbar wasu kudade daga jamiā€™an tsaro ta hanyar da basu kamata ba.


Tsohuwar shugabar kasar taki halartar zaman kotu na yau, wanda alkali ya same ta da laifin karbar Dala miliyan kusan 3 daga cikin kudaden hukumar leken asirin kasa.

Kotun tace ta daure Hye shekaru 6 a gidan yari saboda karbar kudaden da kuma karin shekaru 2 saboda laifuffukan zabe.

Da wannan hukunci na yau, yanzu haka tsohuwar shugabar kasar mai shekaru 66 na fuskantar yin shekaru 32 a gidan yari.

Uwargida Park da aka tsige daga mulki na fuskantar tuhume-tuhume kan cin hanci da rashawa da tozarta karfin mulki da kuma fallasa sirrikan kasa.

Ana zargin Park Geun-hye da hada kai da aminiyarta, Choi Soon-sil wajen karbar kudade daga wasu manyan kamfanonin kasar da suka hada da Samsung da nufin yi mu su alfarmar siyasa.

Koriya ta Kudu na da damar yanke hukuncin rai-da-rai ga duk wanda aka samu da laifin cin hanci da rashawa.