Isa ga babban shafi

Mutane 131 sun bace sakamakon ambaliyar ruwa a Laos

Masu aikin agaji a kasar Laos na cigaba da neman mutanen da suka bace sakamakon fashewar wata madatsar ruwa wadda tayi awon gaba da mutane a cikin gidajen su.

Wasu mazauna kauyen lardin Attapeu, da ambaliyar ruwa ta rutsa da su, a kasar Laos. 24 ga watan Yuli, 2018.
Wasu mazauna kauyen lardin Attapeu, da ambaliyar ruwa ta rutsa da su, a kasar Laos. 24 ga watan Yuli, 2018. ABC Laos News/Handout via REUTERS
Talla

Rahotanni sun ce madatsar ruwar ta fashe ne cikin dare lokacin da dubban mutane ke bacci a cikin gidajen su, abinda ya sa ruwa ya tafi da gidanjen dauke da mutane a ciki.

Ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 20, yayin da wasu 131 suka bace, kamar yadda gwamnatin kasar ta tabbatar, inda ta ce, wasu sama da 3000 kuma suka rasa muhallansu.

Shugabannin Yankin sun mika kokon barar su ga gwamnati da kungiyoyin agaji da su yiwa Allah su taimakawa mutanen su da kayan agaji da suka hada da ruwan sha da abinci da magunguna da kuma kayan sawa.

Wasu hotuna da aka wallafa sun nuna mazauna kauyukan da suka tsira da rayukan su, suna makale akan gidaje domin jiran kai musu dauki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.