Isa ga babban shafi
Pakistan

ISIS ta kashe mutane 31 a ranar zaben Pakistan

Akalla mutane 31 suka rasa rayukansu sakamakon wani kazamin harin kunar bakin wake da kungiyar ISIS ta kaddamar kan jama’a a dai dai lokacin da ake gudanar da zaben game-gari a Pakistan.

Harin wanda ISIS ta dauki alhakin kaddamarwa a Quetta ya hallaka mutane 31 tare da lalata kadarori.
Harin wanda ISIS ta dauki alhakin kaddamarwa a Quetta ya hallaka mutane 31 tare da lalata kadarori. REUTERS/Naseer Ahmed
Talla

Dan kunar bakin waken ya tarwatsa kansa da bama-baman da ya yi damara da su a kusa da rumfar zabe da ke birnin Quetta a ranar Laraba.

Kazalika an samu kanana hare-hare da kuma tarzoma a wasu wuraren daban, abin da ya raunata mutane da dama tare da kashe biyu har lahira.

Miliyoyin mutane ne suka kada kuri’unsu a zaben wanda jam’iyyar tsohon dan wasan Kireket, Imran Khan da ta tsohon Firaminista, Nawaz Sharif ke fafatawa da juna don lashe mafi yawan kujeru.

Mr. Khan ya lashi takobin yaki da cin hanci da rashawa, amma abokin hamayyarsa na zargin cewa, yana samun goyon bayan sojojin kasar da suka mulki Pakistan na tsawon shekaru.

An  garkame Mr. Sharif a gidan yari kan zargin cin hanci da rashawa bayan bankado takardun badakalar Panama da ke nuna yadda attajirai daban daban daga kasashen duniya suka kauce wa biyan haraji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.