Isa ga babban shafi
Pakistan-Imran Khan

Tarihin Imran kan sabon Firaministan Pakistan

Imran Ahmad Khan wanda ke matsayin tsohon Kaftin din tawagar kwallon Kiriket na Pakistan kuma lamba daya a fagen kwallon a duniya an haife shi ne ranar 25 ga watan Nuwamban 1952 kuma shi ne da daya tilo ga mahaifanshi Ikramullah Khan Niazi wani tsohon Injiniyan kasar da shukat Khan.

Tsohon dan wasan kwallon kiriket na Pakistan Imran Khan ya lashe zaben kasar sai dai ba tare da gagarumin rinjaye ba, matakin da ke nuna cewa dole sai ya bukaci hadin kan wasu jam’iyyu don mara masa tafiyar da mulki.
Tsohon dan wasan kwallon kiriket na Pakistan Imran Khan ya lashe zaben kasar sai dai ba tare da gagarumin rinjaye ba, matakin da ke nuna cewa dole sai ya bukaci hadin kan wasu jam’iyyu don mara masa tafiyar da mulki. REUTERS/Athit Perawongmetha
Talla

Imran Khan shi ne shugaban jam’iyyar Pakistan Tahreek Insaf Jam ‘iyyar da dama shi ya kafa ta a shekarar 1996 don tabbatar da adalci da daidaito.

Khan dan Punjabi wanda aka haifa a Pashtun na birnin Lahore ya fara karatu a Aitchison daga bisani ya koma Worcesrter kafin daga baya ya fadada zuwa Kwalejin Keble da ke Oxford .

Tun yana matakin Sakandire a Worcester lokacin ya na da shekaru 13 ya fara bugun Kiriket yayinda ya zama zakakuri a fagen yana da shekaru 18 a duniya musamman bayan wani wasa da ya jagoranta a 1971 a Birmingham.

Bayan kammala digirinsa a Oxford ne kuma, Imran Khan ya koma Pakistan inda ya ke bugawa tawagar kasar kwallon Kiriket tun daga 1976 zuwa 1992 ya kuma rike matsayin Kaftin din tawagar daga shekarar 1982 zuwa shekarar da ya yi ritaya 1992 bayan da ya kai gasar ga gagarumar nasarar lashe kofin duniya na kwallon Kiriket dfin a shekartar.

Bayan ritayarsa daga kwallon Kiriket ne kuma Amir Khan ya assasa wata gidauniyar tallafawa mata masu fama da cutar Cancer a shekarar 1994 inda ya zuba kudi dalar Amurka miliyan 25 wadda ya sadaukar ga mahaifiyarsa.

Imran Ahmad Khan ya rike mukamai daban-daban tun kafin rungumar tafiyar siyasa gadan-gadan, inda aka bashi shugabancin Bradford tun daga 2005 zuwa 2014.

A shekarar 2013 Imran Khan ya tsaya takarar dan majalisar Tarayya ya kuma ci karkashin jam’iyyar da ya assasa a shekarar 1996.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.