Isa ga babban shafi
India-Bangladesh

Mutane miliyan 4 za su rasa shaidar zama Indiyawa

Akalla mutane miliyan 4 na cikin hadarin rabuwa da katinan shidar zama dan kasarsu a jihar Assam da ke arewa maso gabashin India bayanda gwamnati ta fara daukar matakan tantance musulmai ‘yan ciranin da suka tsallako kasar daga Bangladesh.

Tuni dai gwamnati ta girke akalla jami’an tsaro dubu 25 na musamman don kaucewa ballewar rikici, yayinda a bangare guda ake fargabar ballewar zanga-zanga musamman bayanda wasu mambobin majalisar kasar suka bukaci zama na musamman don tattaunawa kan batun.
Tuni dai gwamnati ta girke akalla jami’an tsaro dubu 25 na musamman don kaucewa ballewar rikici, yayinda a bangare guda ake fargabar ballewar zanga-zanga musamman bayanda wasu mambobin majalisar kasar suka bukaci zama na musamman don tattaunawa kan batun. Indranil Mukherjee/AFP
Talla

Sabon shirin tantancewar gabanin bayar da katin dan Kasa a jihar Assam da ke arewa maso gabshin India mai yawan musulmai na da nufin tantance adadin bakin hauren da suka shigo kasar a 1971 yayin yakin ballewar Bangladesh daga Pakistan.

Dama dai tun bayan da Jam’iyyar Firaminista Narendra Modi ta BJP ta ci zabe a jihar ta Assam ta sha alwashin korar ilahirin bakin hauren da ke zaune a jihar ba bisa ka’ida ba, wanda dama na daga cikin alkwarin da ya yi a yakin neman zabe.

Tuni dai gwamnati ta girke akalla jami’an tsaro dubu 25 na musamman don kaucewa ballewar rikici, yayinda a bangare guda ake fargabar ballewar zanga-zanga musamman bayanda wasu mambobin majalisar kasar suka bukaci zama na musamman don tattaunawa kan batun.

Mr Shailesh wanda shi ne babban jami’in Ofishin da ke kula da shirin tantance al’ummar ta Assam ya ce cikin mutane miliyan 30 da suka mika takaddarsu ga ofishin don tantancewa mutane milyan 4 kadai su ke tantamar kasancewarsu Indiyawa.

A cewarsa babu wani abin fargaba matukar mutum yana da hakikanin cewa yana yankin tun kafin 1971 haka zalika akwai damar daukaka kara ga duk wanda ya ke da ja kan hukuncin da aka yanke masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.