Isa ga babban shafi

Amurka ta kakabawa ministan shari'ar Turkiya takunkumi

Kasar Amurka ta sanar da sanya takunkumi akan ministan shari’ar Turkiya da takwaran sa na cikin gida saboda cigaba da tsare wani fasto dan kasar da ake zargi da ayyukan ta’addanci.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Mai Magana da yawun fadar shugaban Amurka, Serah Sanders, tace suna zargin cewar gwamnatin Turkiya na tsare faston Andrew Branson da wata manufa ta dabam.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan yace kasar sa ba za ta bada kai bori ya hau kan barazanar da Amurka ke yiwa kasar sa ba, inda ya zargi kasar da goyan nuna halin Yahudanci.

Fasto Brunson wanda ya shafe sama da shekaru 20 yana aiki a Turkiya, ya fada hannun jami’an tsaron kasar, sakamakon zargin shi da bayar da gudunmawa a yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba, cikin shekarar 2016.

Zalika gwamnatin ta Turkiya na zargin Fasto Brunson da goyon bayan haramtaciyyar jam’iyyar neman ‘yancin Kurdawa ta PKK, wadda shugabancin kasar ta Turkiya ya bayyana tabbacin tana da hannu a yukunrin juyin mulkin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.