Isa ga babban shafi
Indonesia

Mutanen da suka hallaka a girgizar kasar tsibirin Lombok sun karu

Yawan mutanen da suka hallaka sakamakon girgizar kasar da ta sake aukawa tsibirin Lombok na Indonesia, ya karu daga 19 zuwa 32.

Wasu daga cikin gidajen da girgizar kasa ta rusa a tsibirin Lombok na kasar Indonesia.
Wasu daga cikin gidajen da girgizar kasa ta rusa a tsibirin Lombok na kasar Indonesia. Reuters
Talla

Girgizar kasar mai karfin maki 7 a ma’aunin Ritcher, wadda da ta auku a yau Lahadi, ta zo ne mako guda bayan da wata makamanciyarta ta hallaka mutane 17 a tsibirin.

Jami’an gwamnatin Indonesia sun ce an jiyo motsawar girgizar kasar a Tsibirin Bali da ke makwabtaka da tsibirin na Lombok saboda karfinta.

Binciken kwararru ya tabbatar da cewa Indonesia ta fi kowace kasa fuskantar hadarin aukuwar girgizar kasa, aman wuta daga tsaunuka da kuma ambaliya a wasu lokutan, kasancewar ta a yankin Pacific, wadda daga karkashinsa aka fi samun yawaitar motsawar kasa.

A shekarar 2004, wata gagarumar ambaliyar ruwa da girgizar kasa mai karfin maki 9.3 a ma’aunin Richter ta haddasa daga yankin Sumatra da ke yammacin Indonesia, ta yi sanadin salwantar akalla mutane dubu 220,000 da ke zaune a yankunan da ke gaf da tekun India, dubu 168,000 daga cikin wadanda suka hallaka ‘yan kasar Indonesia ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.