Isa ga babban shafi
Iraqi

IS: Kotu ta zartas da hukuncin daurin rai da rai kan wasu turawa

Wata kotun hukunta manyan laifuka a Bagadaza, babban birnin Iraqi, ta zartas da hukuncin daurin rai da rai kan wasu turawa biyu sakamakon samunsu da laifin zama ‘yan kungiyar IS.

Daya daga cikin mayakan IS yayin murnar kame birnin Mosul a ranar 23 ga watan Yuni, 2014.
Daya daga cikin mayakan IS yayin murnar kame birnin Mosul a ranar 23 ga watan Yuni, 2014. REUTERS/Stringer
Talla

Turawan biyu sun hada da Lahcen Gueboutdj mai shekaru 58, Bafaranshe, da kuma wata Bajamushiya da aka bayyana sunanta da Nadia.

A watan Yuli na shekarar 2017, sojin ‘iraqi suka kama Nadia da mahaifiyarta a birnin Mosul, bayan nasarar da dakarun kasar suka samu wajen murkushe mayakan, a lokacin Nadiya tana matsayin matar daya daga cikin ‘yan kungiyar ta IS.

Sai dai a nashi bangaren yayin da kotu ke bayyana hukuncin da ta yanke akansa, Bafaranshe Gueboudji, ya musanta bayanan da ya baiwa jami’an tsaro da farko, inda ya ce tabbas ya yiwa kungiyar ta IS mubaya’a kuma yana karbar horo daga gare su.

Zuwa yanzu dai an yanke hukuncin kisa kan sama da mutane 300 a Iraqi, ciki har da ‘yan kasashen ketare 100, bayan samunsu da lafin zama mayakan kungiyar IS, zalika wasu adadin mutanen kimanin 300, sun fuskanci hukuncin daurin rai da rai.

Kotun hukunta manyan laifukan da ke birnin Bagadaza, ta kuma zartas da hukuncin kisa kan wani dan kasar Iraqi, bayan samun tabbacin cewa dan kungiyar IS ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.