Isa ga babban shafi
Indonesia

Girgizar kasa ta sake afkawa tsibirin Lombok

Girgizar kasa mai karfin maki 5.9 ta sake afkawa tsibirin Lombok na kasar Indonesia a yau Alhamis, karo na uku cikin kasa da makwanni biyu.

Daya daga cikin yankunan yammacin tsibirin Lombok, a Indonesia, da girgizar kasa ta rusa. 6 ga watan Agusta, 2018.
Daya daga cikin yankunan yammacin tsibirin Lombok, a Indonesia, da girgizar kasa ta rusa. 6 ga watan Agusta, 2018. Reuters/路透社
Talla

Lamarin dai ya jefa dubban jama’ar da ke gudun hijira a sansanonin wucin gadi cikin tashin hankali, la’akari da cewa kwanaki hudu da suka gabata wata girgizar kasa mai karfin maki 7 a ma’auninta na Ritcher ta hallaka sama da mutane 160.

Cibiyar bincike al’amuran karkashin kasa ta Amurka ta ce, girgizar kasar ta auku ne a arewa maso yammacin tsibirin na Lombok, a dai dai lokacin da jami’an agaji ke kokarin ceto ragowar wadanda suka rayu daga cikin baraguzan ginin da suka rushe, bayan girgizar kasa mai karfin maki 7 da ta afkawa tsibirin a ranar Lahadi, 5 ga watan Agusta na 2018.

Wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa ya rawaito cewa, girgizar kasar ta yau Alhamis ta jefa matukar tsoro a zukatan mazauna tsibirin, inda a lardin Tanjung mutane suka rika ficewa daga ababen hawansu akan tituna suna guje guje cikin dimuwa.

Kakakin hukumar bada agajin gaggawa ta Indonesia Sutopo Purwo Nugroho ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa, mutane 164 suka rasa rayukansu a girgizar kasar da ta auku a ranar Lahadin da ta gabata.

Nugroho ya kara da cewa mutane 1, 400 suka jikkata yayinda girgizar kasar ta raba sama da mutane dubu 150, 000 da muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.