Isa ga babban shafi
China

China na tsare da Muslmi miliyan 1 a boyayyun sansanoni - MDD

Kwamitin yaki da wariya da kuma cin zarafin dan adam na majalisar dinkin duniya, ya ce gwamnatin China na tsare da Muslmi mafi akasari ‘yan kabilar Uighur da na wasu kabilun marasa rinjaye akalla miliyan daya, a wasu sansanonin tsare wadanda ake zargi da tsattsauran ra’ayi.

Jami'an tsaron China yayin sintiri a garin Kashgar, na Lardin Uighur, yayin da Muslmi ke fitowa daga Masallaci bayan kammala ibada.
Jami'an tsaron China yayin sintiri a garin Kashgar, na Lardin Uighur, yayin da Muslmi ke fitowa daga Masallaci bayan kammala ibada. AFP
Talla

Kwamitin, ya wallafa rahoton nasa ne a ranar Juma’a, bayan soma bincike kan zarge-zargen da ake yiwa gwamnatin China na cin zarafin dan adam, musamman akan Musulmi.

Rahoton ya kara da cewa an kuma tilastawa wasu karin Muslmin miliyan biyu, a lardin na Uighur, shiga wasu sansanonin sauya musu alkibila ta fuskokin ilimi, siyasa da kuma al’adu.

Wani karin bayani cikin rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya ce jami’an tsaron China sun tsare Musulmi ‘yan kabilar Uighur sama da 100 baya da suka koma gida daga karatu a kasashen Masar da Turkiya, kuma mafi akasarinsu sun hallaka yayin da suke tsare a kurkuku, abinda ya sa ake zargin cewa an azabtar da su ne.

Kwamitin majalisar dinkin duniyar ya kuma ce, hukumomin tsaron China, sun cin zarafin wadanda ke amfani da sallamar Musulmi a matsayin gaisuwa, da cin abincin halal kawai.

Zalika ana zargin hukumomin na China da cin zarafin Musulmi da ke baring emu da mata masu amfani da Hijabi ko dan kwali.

A ranar Litinin mai zuwa kwamitin yaki da wariyar na majalisar dinkin duniya zai cigaba da nazari kan zarge-zargen tauye hakkin da ake yi wa China.

Gwamnatin China ta dade tana da’awar cewa yankin Uighur ko Xinjiang, yana fuskantar barazana daga wasu gungun ‘yan tawaye da ‘yan aware da ke haddasa tashin hankali tsakanin Muslmi ‘yan kabilar ta Uighur marasa rinjaye da kuma kabilar Han masu rinjaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.