Isa ga babban shafi
Syria

Rayukan fararen hula 53 sun salwanta a Syria

Jami’an da ke sa ido kan yakin Syria, sun ce fararen hula 53 cikinsu har da kananan yara 28 sun hallaka, a hare-haren da jiragen yaki suka kai kan wasu yankunan ‘yan tawayen dake arewacin kasar.

Wasu kananan yara da suka rasa muhallansu a yakin Syria, a wani sansani da ke kan iyaka ta Turkiya a lardin Idlib. 17, Janairu, 2018.
Wasu kananan yara da suka rasa muhallansu a yakin Syria, a wani sansani da ke kan iyaka ta Turkiya a lardin Idlib. 17, Janairu, 2018. REUTERS/Osman Orsal
Talla

Da fari dai lokacin da aka kai harin a ranar Juma’ar da ta gabata, jami’an sun ce fararen hula 30 ne suka hallaka, amma daga bisani sun ce fararen hula 41 ciki harda yara 25, suka hallaka a garin Orum al-Kubra da ke gaf da lardin Aleppo, yayinda wasu fararen hular 12 uku daga cikin yara suka rasa rayukansu a Idlib.

Har yanzu mafi akasarin lardin Idlib yana karkashin ‘yan tawayen Syria, sai dai shugaban kasar Bashar al-Assad ya yi gargadin cewa da zarar ya gama da ‘yan tawayen da ke makwabtaka da birnin damakas zai juya kan lardin na Idlib.

Lardin Idlib mai yawan jama’a da suka kai akalla miliyan biyu da rabi, na daga cikin yankunan da aka haramta kai hare-haren a yakin Syria, karkashin wata yarjejeniya da aka cimma tsakanin masu ruwa da tsaki a yakin kasar da suka hada da Rasha, Syria, Amurka da kuma sauran kungiyoyin mayakan sa kai da na ‘yan tawaye.

Bayan shafe shekaru bakwai ana gwabza yaki a Syria da aka soma a shekarar 2011, zuwa yanzu sama da mutane dubu, 350,000 ne suka hallaka, yayinda wasu miliyoyi suka rasa muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.