Isa ga babban shafi
Myanmar

Myanmar ta bukaci daina baiwa 'yan kabilar Rohingya agaji

Gwamnatin Myanmar ta bukaci kasar Bangladesh da dakatar da kai kayan agaji ga ‘yan kabilar Rohingya Musulmi kusan 6,000 da yanzu haka suka makale akan iyakar kasashen biyu, bayan kazamin harin da sojojin kasar suka kai ya tilasta musu tserewa daga gidajensu.

Wasu kananan yara 'yan kabilar Rohingya, yayin da suke bin layin karbar abinci a sansanin Kutupalong, bayan tserewa daga Myanmar zuwa Bangladesh.
Wasu kananan yara 'yan kabilar Rohingya, yayin da suke bin layin karbar abinci a sansanin Kutupalong, bayan tserewa daga Myanmar zuwa Bangladesh. AFP
Talla

Myanmar ta yi kiran ne lokacin tattaunawa tsakanin ministan harkokin wajen Bangladesh A.H . Mahmood Ali da babban jami’in diflomasiyar Myanmar Kyaw Tint Swe a ganawar da suka yi a Napyidaw, babban birnin kasar ta Myanmar.

Yawan ‘yan kabilar Rohingya da suka tsere daga Myanmar don gujewa cin zarafin sojin kasar a jihar Rakhine ya zarta dubu 700,000, a dalilin yi musu kisan gilla, fyade ga matansu da kuma sauran nau’o’in azabtarwa.

Sai dai a cewar gwamnatin kasar a sojin kasar na kokarin murkushe masu tada kayar baya ne daga cikin ‘yan kabilar ta Rohingya, wadanda suka hadda barkewar rikici a jihar ta Rakhine cikin shekarar 2017.

Ma’aikatar harkokin wajen Myanmar tace gwamnatin kasar ta bukaci Banglashe da ta daina tura kayan agaji ga mutanen, inda ta bayyana shirin gabatar musu da agaji daga gida.

Koda yake gwamnatin Bangladesh ba ta amsa bukatar daina baiwa ‘yan gudun hijirar na Rohingya kayan agaji ba, ministan harkokin wajen kasar Mahmood Ali ya amince da bukatar yin rangadin fadin kasar da a yanzu ‘yan kabilar ta Rohingya ke zaune suna gudun hijira.

A baya dai gwamnatin Myanmar ta gargadi ‘yan gudun hijirar da su gaggauta amsa tayinta na mayar da su gida, idan suka saba kuma, su kuka da kansu, kan duk abinda ya biyo baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.