Isa ga babban shafi
Philippines

Guguwar Mangkhut ta yi ta'adi a kasashen Asiya

Mahaukaciyar guguwar da masana suka yi wa lakabi da Mangkhut ta yi mummunan ta’adi a Hong Kong da kuma wasu sassa na kasar China, bayan ta kashe dimbin mutane a kasar Philippines. Kafin isar guguwar, tuni mahukunta a China suka kwashe sama da mutane milyan 3 daga yankin kudancin kasar.

Guguwar Mangkhut ta share gidaje da dama tare da kashe mutane sama da 60 a Philippines kadai
Guguwar Mangkhut ta share gidaje da dama tare da kashe mutane sama da 60 a Philippines kadai REUTERS/Harley Palangchao
Talla

Kawo yanzu an kiyasta cewa guguwar ta yi sanadiyyar mutuwar mutune 65 a Philippines kawai, yayin da ta tilasta wa mahukunta daukar matakin kwashe mutanen da yawansu ya kai milyan uku daga yankin kudancin kasar China.

Mahaukaciyar guguwar ta fi yin ta’adi ne a tsibirran Luzon da kuma Itogon da ke Philippines, in da yanzu haka ake ci gaba da gano gawarwarkin mutane daga cikin tabo da kuma rafuka.

Guguwar ta share mafi yawan garuruwan da ke wadannan tsibirai biyu, kafin daga bisani ta isa cikin kasar China a marecen ranar Lahadi, in da rahotanni ke cewa ta kashe mutane da dama a lardin Guangdong.

An rufe dimbin makarantu a lardin tare da hana zirga-zirgar motoci da ma jiragen kasa, sakamakon yadda guguwar ta karya manyan itace da kuma toshe hanyoyin layin dogo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.