Isa ga babban shafi
Korea

Ganawar shugabannin kasashen Koriya ta yi kyau

Shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-in ya bayyana ganawar da suka yi da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un da cewa ta haifar da sakamako mai kyau, domin kuwa takwaransa ya tabbatar da cewa zai rufe wasu daga cikin cibiyoyin bincike da kuma na harba makaman nukiliyar kasar nan ba da jimawa ba.

Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un da takwaransa na Koriya ta Kudu, Moon Jae In
Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un da takwaransa na Koriya ta Kudu, Moon Jae In Pyeongyang Press Corps/Pool via REUTERS
Talla

A zantawarsa da manema labarai a ranar Laraba, shugaba Moon Jae-in ya ce, ya samu tabbaci daga Kim Jong Un cewa, Koriya ta Arewa za ta rufe babbar cibiyar da take amfani da ita don gwajin makaman nulilya da ake kira Tongchan-ri, kuma za a rufe ta ne gaban idon kwararri na kasashen duniya.

Har ila yau Koriya ta Arewa ta ce, za ta rufe wata cibiyar bincike kan makaman na nukilya da ke Yongbyon, amma da sharadin cewa Amurka za ta cika wa kasar wasu alkawurra da bai fayyace ba.

A lokacin ganawar, shugabannin kasashen biyu sun ce za su ci gaba da aiwatar da shirin bai wa iyalan da aka raba tsawon shekaru damar saduwa da juna, yayin da Kim Jong Un ya ce, zai kai ziyara a birnin Seoul watakila kafin karsehn wannan shekara.

Wasu batutuwan da shugabannin suka tattaunawa a ganawar da suka yi a ranar Talata kuwa sun hada da gina hanyoyin mota da kuma layin dogo da za su hade kasashensu biyu wadanda ke fatan samun damar daukar nauyin shirya wasannin Oplympics a 2032 mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.