Isa ga babban shafi
Faransa-Falestinawa

Abbas da Macron na neman tallafawa Falasdinawa

Bayan ganawar da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas da shugaban Fransa Emmanuel Macron a Paris, domin tattauna sake farfado da shirin samar da zaman tskanin su da Isra'ila, sun amince da shirya taron neman tallafi kudade ga hukumar yan gudun hijrar Falestinawa ta M ajalisar Dinkin Duniya UNRWA bayan da Amruka ta rage yawan tallafin kudin da take bata.

shugaban Faransa Emmanuel Macron da na Falestinawa Mahmoud Abbas. 21/09/18
shugaban Faransa Emmanuel Macron da na Falestinawa Mahmoud Abbas. 21/09/18 REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Mako guda kafin gabatar da jawabinsa ga komitin tsaro na MDD, a birnin New York, a yau juma’a 21 ga watan satumba 2018, shugaban al’umar Palestinawa Mahmoud Abbas ya ziyarci birnin Paris, inda ya gana da shugaban kasar Emmanuel Macron a fadar Elysée, bayan ganawar farko da suka yi a watan desemba shekara ta 2017 inda a wanan lokacin shugaban na Faransar ya bayyana goyon bayansa ga Flaesinawa

Tun bayana amincewa da birnin na kudus a matsayin babban birnin Israela da Amruka ta yi a 2017 ne, Shugaban Falestinawa Mahmud Abbas, ya kauracewa duk wata tattaunawar diflomasiya da Amurka, tare da zargin ta da goyon bayan Izraela kirikiri

Tun daga wannan lokaci dai falastinawa da dama dake zanga zangar nuna rashin amincewa da matakin na Amruka, da kuma mamayen yan kakagidan yahudawa ne dakarun izraela suka harbe har lahira tare da jikkata wasu daruruwa

Ko a ‘yan makwanin da suka gabata, gwamnatin Amruka ta sake daukar wasu jerin takunkuman ladaftarwa kan hukumar ta falastinawan, da nufin tilasta mata shiga tattaunawa neman zaman lafiya da Isaraelar

Matakan da suka hada da rufe ofishin jakadancin kungiyar falestinawa PLO dake Washington, da kuma zaftare kaso mafi yawa na kudaden tallafin da take baiwa kasafin kudin Falestinawan

za a iya cewa dai, ganawar tsakanin shugaban Faransa da na Faslestinawan na da matukar muhimmanci, domin zata bada damar shirya zaman taron neman gudummuwar kudi a karkashin MDD ga yan gudun hijirar alestinawan wajen wajen cike gibin da Amrukar ta haifar masu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.